
Farfesa Rhoda Gumus, kwamishiniyar zabe ta kasa dake lura da jihar Edo tayi alkawarin cewa baza ta karbi cin hanci da rashawa ba a zaben Gwamnan jihar dake gudana yanzu haka.
Daily Trust ta rawaito cewa Gumus ta yi bayanin hakan ne a yayin tattaunawa da Channels TV.
Ta sha alwashin cewa ba wanda ya isa ya tunkaret da maganar cin hanci saboda kimar ta.
Kwamishiniyar zaben ta kara da cewa za a fara tantance masu zabe da karfe 8 inda ta ce ana sa ran kammala zaben da karfe 2 na rana amma duk wanda aka tantance za a bashi damar yin zaben.
Tayi alkawarin cewa zaben na jihar Edo zai zama mafi inganci da INEC ta gudanar.
Gamus ta ce, “Ni ce ke kula da Edo. Ina son yin abinda yake daidai duk da cewa bazan kasance a ko-ina ba. Zamu yi zaben nan cikin adalci. Bazan karbi toshiyar baki ba ko nawa ne. Ba sai na karbi Biliyoyin kudi zan yi abinda yake daidai ba.
“Ba wanda ya isa ya gwada ni”, inji ta.