
Gwamnatin jihar Adamawa a yau Lahadi ta tabbatar da barkewar cutar kwalara tare da hallaka mutane 12.
Kwamishinan lafiya na jihar, Felix Tangwami, wanda ya tabbatar da ɓarkewar cutar a cikin wata sanarwa a Yola, ya ce daga cikin samfura 50 da ake zargin sun kamu da cutar, 30 sun kamu da cutar.
Tangwami ya ce shida daga cikin wadanda suka mutu a asibiti ne, shida kuma a gida yayin da aka kwantar da kusan mutane 308 tare da 244 da aka yi musu magani kuma aka sallame su.
“A madadin Gwamnan Jihar, ina so in sanar da ku duk cewa mun samu sakamakon samfurori da aka aika wa hukumar NCDC don tabbatarwa, an tabbatar da ɓarkewar Kwalara a jihar mu.
“Abin takaici, daga cikin samfurori 50 da aka aika zuwa dakin gwaje-gwaje na Cibiyar Gwaje-gwajen Lafiya ta Ƙasa (NRL) da ke Abuja, samfurori 30 sun nuna akwai cutar kwalara, shida kuma sun nuna babu, biyu kuma ba a kammala ba, sannan 12 har yanzu sun makale.