Home Labarai YANZU-YANZU: Kotu ta kori karar da ke neman a cire Ganduje daga shugabancin APC na kasa

YANZU-YANZU: Kotu ta kori karar da ke neman a cire Ganduje daga shugabancin APC na kasa

0
YANZU-YANZU: Kotu ta kori karar da ke neman a cire Ganduje daga shugabancin APC na kasa

Wata babbar kotun tarayya da ke Abuja ta kori ƙarar da aka shigar gaban ta, ake neman ta sauke Abdullahi Umar Ganduje daga shugabancin jam’iyyar APC ta kasa.

Mai shari’a Inyang Ekwo, a hukuncin da ya yanke ya kori karar bisa dalilin cewa wanda ya shigar da korafin, shugaban kungiyar APC na Arewa ta tsakiya, Saleh Zazzaga basu da hurumin shigar da ita.

Mai shari’a Ekwo ya ce babu wata shaida da aka gabatar na cewa kungiyar tana da rijista da CAC, ya ce doka bata san da sunan kungiyar ba.

Alkalin ya ce za a iya cire shugaban jam’iyya ko nada shi ne kadai ta hanyar babban taron jam’iyyar na kasa.

Kodayake, lauyan kungiyar, Ayuba Abdul ya shaidawa manema labarai cewa zasu daukaka kara kan hukuncin.