
Gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Zulum ya ce kawo ya zu, kuɗin da su ka shiga asusun jihar na tallafawa wadanda ambaliyar ruwa ta shafa a jihar bai wuce Naira biliyan N4.4 ba.
Daily Trust ta rawaito cewa gwamnatin jihar dai ta bude asusun domin tallafa wa wadanda ambaliyar ruwan ta shafa.
Rahotanni sun nuna cewa kuɗin da aka tara na gudummawa ya kai Naira biliyan 13.
Sai dai kuma Zulum ya baiyana cewa Naira biliyan 4.4 kawai su ka shigo asusun.
“Mun samu alkawari na Naira Biliyan 13, 500, 000; kodayake daga jiya Lahadi, mun karbi jimillar kudi Naira Biliyan 4, 4441, 494, 902.81. Duk abinda aka tura wannan asusun za mu sanar da al’umma,x in ji Zulum.
Gwamnan, wanda ya bayyana hakan yayin da yake kaddamar da kwamitin mutane 35 na rabba tallafin rage radadin a birnin Maiduguri a ranar Litinin, ya bukaci mambobin kwamitin su yi aikin da gaskiya.
” Dole ne mu yi taka-tsantsan da dukkan abinda aka bamu”, inji shi.
Gwamna Zulum ya kara da cewa, “Dole ne mu tabbatar da an yi amfani da duk Naira daya da aka bayar don rage radadi ta isa ga wadanda abin ya shafa”
Gwamnan ya kuma umarci a biya kudin alawus na mambobin daga asusun gwamnatin Borno ba asusun tallafin ba.
Gwamnan ya umarci a bada tallafin dukkan sa ga wadanda ambaliyar ta shafa.
Daidaiku da kungiyoyi ne dai suka bada gudunmawa ga wadanda iftila’in na Maiduguri ya shafa.