Home Labarai Lokaci ya yi da gwamnati za ta kawo karshen biyan tallafin man fetur — Dangote

Lokaci ya yi da gwamnati za ta kawo karshen biyan tallafin man fetur — Dangote

0
Lokaci ya yi da gwamnati za ta kawo karshen biyan tallafin man fetur — Dangote

Mamallakin matatar mai ta Dangote, Aliko Dangote, ya ce lokaci ya yi da gwamnatin tarayya za ta kawo karshen biyan tallafin man fetur.

A yayin tattaunawa da jaridar Bloomberg a ranar Litinin, Dangote ya ce tallafin mai zai kai gwamnati ga “Biyan abinda bai kamata ta rika biya ba” don haka akwai bukatar kawo karshen sa.

Daily Nigerian ta rawaito cewa dan kasuwar ya jadadda cewa gwamnatin Tinubu baza ta iya jure biyan tallafin man ba.

Dangote ya ce: “Ina tunanin yanzu ne lokacin janye tallafin mai sabora duk kasashe sun dena biyan tallafin.

” Gwamnati baza ta iya biyan tallafin mai ba,” in ji shi.