Home Labarai Labarin Samoa: Kun tafka kuskure — Kwamitin sa ido kan aikin jarida ya tabbatarwa Daily Trust

Labarin Samoa: Kun tafka kuskure — Kwamitin sa ido kan aikin jarida ya tabbatarwa Daily Trust

0
Labarin Samoa: Kun tafka kuskure — Kwamitin sa ido kan aikin jarida ya tabbatarwa Daily Trust

Kwamitin karɓar Ƙorafe-ƙorafe kan Kafafafen Yaɗa Labarai na Kasa (NMCC), ya fitar da rahotonsa kan taƙaddamar zargin goyon bayan auren jinsi Yarjejeniyar da gwamnatin tarayya ta sanyawa hannu ta Samoa.

Kwamitin wanda gogaggun yan jarida da lauyoyi ke yiwa shugabanci ya ce kamfanin Daily Trust ya tafka kuskure a wancan labarin akan Yarjejeniyar ta Samoa.

Binciken ya biyo bayan korafin da Ma’aikatar Yada Labarai da Wayar da Kan Jama’a ta Tarayya ta yi a kan jaridar Daily Trust.

Hukumar, a cikin rahotonta mai shafuka 19, ta ce bayan ta binciki korafin gwamnati, da kuma martanin da jaridar tayi, ta gano labarin da jaridar Daily Trust ta wallafa kan yarjejeniyar SAMOA a matsayin kuskure, tare da umartar Jaridar ta nemi afuwar Gwamnatin Tarayya bisa abin da rahoton na su ya jawo mata.