
Rundunar Ƴansanda a jihar Legas ta ce tana tsare da wani mutum mai shekaru 30 , Motunrayo Olaniyi bisa zargin daɓawa amaryar sa wuka, Olajumoke mai shekaru 25 wacce ta rasa ran ta.
Mai magana da yawun rundunar, SP Benjamin Hundeyin, ne ya tabbatar da faruwar lamarin ga kamfanin dillancin labarai na kasa a birnin Legas.
Ya ce lamarin ya faru ne a ranar Juma’a da misalin karfe 1 na rana a yankin Ikorodu na jihar.
Hundeyin ya ce ofishin ƴansanda na Ikorodu ya samu kira kan faruwa lamarin.
“Ofishin ‘yansanda na Ikorodu ya samu kira kan cewa wasu sabbin ma’aurata sun samu rikici a dakin su, a inda yayin ce-ku-ce kuma mijin ya kashe matar.
” Ya kulle ta a dakin sannan ya cinna wuta a yayin da ya jiwa kansa ciwo”, inji Kakakin ‘yansandan.
Mai magana da yawun ‘yansandan yace jami’an sun isa wurin.
Sannan ya ce a yayin da jami’an suka shiga wurin, an yi kokari an kashe wutar tare da dakko gawar matar.
Acewarsa, ana ci gaba da bincike kan lamarin.
D