
Hajiya Sa’adatu Salisu Yushau, zaɓaɓɓiyar shugabar ƙaramar hukumar Tudunwada ta karbi rantsuwar kama aiki.
Hajiya Sa’adatu na daya daga cikin ciyamomi 44 da gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf ya rantsar a yau Asabar a gidan gwamnatin jihar.
A hirar ta da wakilin DAILY NIGERIAN HAUSA, Hajiya Sa’adatu ta ce kasancewar ta mace ɗaya tilo kuma ta farko a tarihin jihar Kano da ta zama shugabar ƙaramar hukuma, za ta yi kokari ta ciyar da Tudunwada gaba.
A cewar ta, “duk abinda namiji zai iya mace ma za ta iya”, saboda haka ta ce za ta dage ta ga ta yi bajintar da ba a taba yi ba a ƙaramar hukumar Tudunwada.
Ta ce ta ma da yaƙinin da taimakon Allah da kuma daukacin al’ummar Tudunwada, za ta sauke nauyin da aka dora Mata wajen inganta rayuwar al’ummar yankin.