
Sabon Shugaban Ƙaramar Hukumar Fagge, Salisu Usman Masu ya baiyana takaici kan yadda ya ce ana karkatar da kusan kashi 90 na kuɗaɗen shigar ƙaramar hukumar.
A wata hira da wakilin Daily Nigerian Hausa jim kadan bayan ya karbi shaidar lashe zabe a yau Lahadi , Masu ya ce kuɗaɗen aljihun tsirari ya ke shiga.
A cewar sa, lamarin ya kai ga ƙaramar hukumar ta Fagge ba ta iya biyan ma’aikata albashi daga kaso da gwamnatin taraiya ke bata na wata-wata har sai gwamnatin jiha ta cika mata.
Masu ya kara da cewa lamarin abin takaici ne duba da cewa ƙaramar hukumar Fagge ta fi kowacce hanyoyin samun kuɗaɗen shiga a jihar Kano saboda kasuwanni da sauran guraren kasuwanci da ke yankin na ta.
Ya ci alwashin magance wannan ta’adda da zarar ya kama aiki, inda ya yi alƙawarin ” toshe duk wata hanya da kuɗaɗen shiga ke zurarewa don samun damar yi wa al’umma aiyukan raya ƙasa.”
Ya kuma baiyana cewa gyaran harkar ilimi da tallafawa matasa da mata shine babban muradin sa idan ya kama aiki a matsayin shugaban ƙaramar hukumar ta Fagge.