
Kotun Ɗaukaka Ƙara a Abuja ta yi kori wasu roƙo guda uku da Aminu Babba Dan’agundi ya shigar gaban ta saboda rashin cancanta.
Dan’agundi ya shigar da roƙon ne domin gyara wasu kura-kurai a bayanan sa na daukaka ƙara.
Daily Trust ta rawaito cewa a dalilin haka, kotun ta ci tarar Dan’agundi Naira dubu 500 kan ko wanne roko, inda ta kama Naira miliyan ɗaya da dubu 500 kenan.
Hakazalika Daily Trust ta rawaito cewa kotun ta tanadi Ranar yanke hukunci akan ƙara guda huɗu a cikin gida shida da aka shigar bisa dambarwar masarauta.
Kwamitin alkalai uku, ƙarƙashin jagorancin Mai Shari’a Mohammed Mustapha ne ya tanadi ranar yanke hukuncin bayan da lauyoyin ɓangarori biyun su ka yi muhawara a kan daukaka karar.
Lauyoyin da su ka yi muhawarar sun hada da na gwamnatin Kano, Adegboyega Awomolo (SAN) da na Majalisar Dokokin Kano , Okechukwu Edeze (SAN) wanda ya roki kotu da ta yi duba da tabbatar da daukaka karar su, sai kuma kayan wadanda ake ƙara, P.H. Ogbole (SAN) wanda ya roki kotun da ta yi watsi da ƙarar.
A tuna cewa babbar kotun tarayya da ke zaman ta a Kano, karkashin Mai Shari’a Abdullahi Liman ta soke nadin da gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf ya yi wa Sarki Muhammadu Sanusi ko a matsayin Sarkin Kano na 16 a ranar 23 ga watan Mayu, lamarin da ya sanya ta garzaya kotun daukaka kara a Abuja.