
Tsohon shugaban kwamitin riko na jam’iyyar APC, kuma tsohon Gwamnan jihar Legas Cif Bisi Akande, ya bayyanawa manema labarai a ranar alhams cewar, har zuwa wannan lokacin babu wani mutum da APC ta ayyana a matsayin dan takarar ta na shugaban kasa. Yace Shugaban kasa Muhammadu Buhari, bai bayyana musu aniyarsa ta yin takara ba.
A dan haka, Cif Akande, yace kowanne dan jam’iyya yana da iko da kuma ‘yancin tsayawa takara a zaben 2019 da yake tafe. Ya kara da cewar, ko da Buhari zai sake neman tsayawa zabe, to dole ne zai yi takara tare da wasu a cikin jam’iyyar, ma’ana ba shi kadai za’a sahalewa tsayawa takara ba.
Bisi Akande ya bayyana hakan ne a taron masu ruwa da tsaki na jam’iyyar APC daga yankin kudu maso yamma, ya kara da cewar, har wannan lokacin Shugaba Buhari bai bayyanawa shugabannin yankin kudu maso yamman ko zai tsaya zabe ko ba zai tsaya ba.
Da aka tambaye shi ko jam’iyyar zata iya sahalewa Shugaba Buhari kara tsayawa zabe ko a’a, ya bayar da amsa da cewar, wannan ba abu bane na gaggawa, yace jam’iyya zata bayyana hakan a lokacin da ya dace, amma dai har yanzu Buhari bai nuna sha’awarsa ta tsayawa takara ba, a cewar Cif Bisi Akande.
A dan haka, tun da Shugaba Buhari bai bayyana mana kko zai tsaya zabe ba, to kowanne dan jam’iyya na da ikon nuna sha’awarsa ta tsayawa takarar shugaban kasa a jam’iyyar APC.