
Kakakin Majalisar wakilai ta kasa Yakubu Dogara zai sake tsayawa takarar dan Majalisar wakilai mai wakiltar Dass da Bogoro da Tafawa Balewa a karkashin tutar jam’iyyar PDP.
Dogara dai bai bayyana ficewarsa daga jam’iyyar APC ba sai yanzu da ya sayi takardun tsayawa takara a karkashin jam’iyyar PDP.