
A kasar Kamaru An sake zaben Paul Biya dan shekaru 85 a matsayin Shugaban kasa karo na 7 a jere.
Tuni dai hukumar zaben kasar ta bayyana Shugaba Biya a matsayin wanda ya lashe zaben Shugaban kasar wanda yayi Nasara da kashi 71.2.
Amma jagoranci ‘Yan adawa kasar a birnin Yawunde da Duwala sun yi kira da a soke zaben kuma a sake yinsa. Abinda hukumar zaben kasar tayi fatali da shi.