Home Labarai ‘Yan bindiga sun yi garkuwa da wasu tagwaye a Zamfara

‘Yan bindiga sun yi garkuwa da wasu tagwaye a Zamfara

0
‘Yan bindiga sun yi garkuwa da wasu tagwaye a Zamfara

Rahotanni daga garin Daura a yankin karamar hukumar mulki ta Zurmi a jihar Zamfara na nuna cewar wasu ‘Yan bindiga sun yi garkuwa da wasu tagwaye mata a jihar.

Bayanai sun nuna cewar an sace ‘Yan matan ne tare da yin garkuwa da su a yayin da suka fita zuwa kai dinkin bikinsu da za ai nan gaba kadan.

’Yan bindigar dai sun nemi a basu kudin fansa kafin su saki wadannan ‘Yan tagwaye. Wakilinmu ya kira lambar wayar kakakin rundunar ‘Yan sanda ta jihar Zamfara amma bata shiga.