
Ministan yada labarai da al’adu Alhaji Lai Mohammed ya bayyana cewar Gwamnatin tarayya na kashe zunzurutun kudi Naira miliyan uku da dubu dari biyar wajen ciyar da shi a duk wata.
Idan ba a manta ba tun a watan Disambar shekarar 2015 Gwamnatin tarayya ya kama Zakzaky tare da garkame shi bayan da aka samu hatsaniya tsakanin mahiyansa da kuma rundunar sojojin Najeriya.
Tun lokacin gwamnati ke tsare da Zakzaky tare da matarsa Zinatu.