Home Labarai Shugaban kasa Buhari ya isa Sakkwato don ta’aziyar Shagari

Shugaban kasa Buhari ya isa Sakkwato don ta’aziyar Shagari

0
Shugaban kasa Buhari ya isa Sakkwato don ta’aziyar Shagari

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya isa jihar Sakkwato domin yin ta’aziyar rasuwar tsohon Shugaban kasa Shehu Usman Aliyu Shagari.

Allah ya yiwa tsohon Shugaban kasa Shehu Shagari rasuwa a ranar Juma’a, wanda aka yi jana’izarsa ranar Asabar da safe a karamar hukumar Shagari dake jihar Sakkwato.