Home Kanun Labarai Aisha Buhari ta kaddamar da yakin neman zaben Buhari a Kano

Aisha Buhari ta kaddamar da yakin neman zaben Buhari a Kano

0
Aisha Buhari ta kaddamar da yakin neman zaben Buhari a Kano

Uwar gidan Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kaddamar da yakin neman sake zaben Shugaba Buhari a karo na biyu a karkashin tutar jam’iyyar APC.

Hajiya Aisha Buhari ya kaddamar da gangamin taron a shiyyar Arewa maso yamma wanda aka yi a birnin Kano. Taron ya samu halartar Gwamnan jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje da uwar gidansa Hajiya Hafsah Ganduje.