Home Labarai Karon battar ‘yan Shiah da ‘yan sanda a Kano ta bar baya da kura

Karon battar ‘yan Shiah da ‘yan sanda a Kano ta bar baya da kura

0
Karon battar ‘yan Shiah da ‘yan sanda a Kano ta bar baya da kura
'Yan Shiah yayinda suka fito zanga zanga a birnin Kano

kakakin kungiyar ‘yan Shiah Ibrahim Musa ya shaidawa manema labarai cewar, a sakamakon karon battar da aka yi a ranar Lahadi tsakanin ‘yan Shiah da ‘Yan Sanda a birnin Kano ya bar musu baya da kura. Domin a cewarsa,mabiya Shiah mutum biyu ne aka hallaka a yayin arangamar.

An yi wannan arangama ne a ranar lahadin da ta gabata a cikin birnin Kano, lokacin da ‘yan Shiah suka fito domin fara yin wani tattaki da suke yi duk shekara zuwa garin Zaria a kafa,sai dai a bana abin ya sha bamban, kasancewar an rusa guraren ibadar tasu tun a arangamar da suka yi da sojoji.

A bana sun fito tattakin ne domin zagawa a cikin birni inda suke dauke da kwalaye na kiraye kiraye da a saki Shugabansu Ibrahim Yakubu El-zakzaky. Daga cikin mutum biyun da aka kashe, har da wata daliba dake karatu a jami’ar Bayero dake Kano.

Sai dai kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Kano, Magaji Musa Majiya, ya ce har ya zuwa yanzu, bai samu cikakken abinda ya auku tsakanin jami’ansu da kuma mabiya Shiah ba. Sai dai yace, yana da masaniyar cewar, rundunar tasu ta gargadi ‘yan shiah akan wannan tattaki da suka kuduri yinsa a ranar lahadin.

Wannan tattaiki dai da ake kira Arba’in yana daga cikin bukuwan mabiya Shiah na tunawa da mutuwar Sayyadi Hussain Bin Aliyu Ibn Abi-Talib, wanda suke cewar suna juyayin rasuwarsa.