Home Siyasa 2023: Abba Gida-gida ya barranta kansa da buɗe asusun tallafin takararsa

2023: Abba Gida-gida ya barranta kansa da buɗe asusun tallafin takararsa

0
2023: Abba Gida-gida ya barranta kansa da buɗe asusun tallafin takararsa

 

 

 

 

Dan takarar gwamna na jam’iyyar NNPP, Abba K. Yusuf ya nisanta kansa daga buɗe wani asusu na tallafa wa takararsa ta gwamnan Kano a 2023.

A cikin wata sanarwa da mai magana da yawunsa, Sanusi Bature Dawakin-Tofa ya fitar a yau Talata a Kano, Yusuf, wanda magoya bayansa ke kira Abba Gida-gida, ya ce an ja hankalinsa a kan wata bidiyo da ake yaɗa wa, cewa ya ƙaddamar da asusun tallafi na takararsa.

A cewar sanarwar, bidiyon da ake yaɗa wa ta nuna cewa Abba Gida-gida na neman tallafin Naira dubu ɗaya-ɗaya, inda ya ce wannan zancen ƙarya ne.

Ya ƙara da cewa wannan batun wani aiki ne na ƴan adawa, waɗanda su ke so su dakushe farin jininsa da na jam’iyar NNPP.

A cewar Abba Gida-gida, shi ƙungiya ɗaya ya sani, mai suna Friends of Abba Gida-gida, wacce abokai ne da yan uwa su ka haɗa domin nuna goyon bayansu ga takararsa.

A karshe dai Abba Gida-gida ya yi kira ga masoya da ƴan jam’iyyar NNPP da su yi watsi da wannan labarin a matsayin ƙarya da yarfe.