Home Siyasa Abdul-Azeez Jandor ya lashe tikitin takarar gwamna na PDP a Legas

Abdul-Azeez Jandor ya lashe tikitin takarar gwamna na PDP a Legas

0
Abdul-Azeez Jandor ya lashe tikitin takarar gwamna na PDP a Legas

 

 

 

 

A jiya Larabar ne dai Jagoran Ƙungiyar Lagos4Lagos, Abdul-Azeez Olajide Adediran (Jandor) ya lashe tikitin takarar gwamna na jam’iyyar PDP a zaɓen 2023 a Jihar Legas.

Da yake bayyana sakamakon a Ikeja, Shugaban Kwamitin Zaɓe na PDP na Legas, Emmanuel Ogidi, ya ce Adediran ya samu ƙuri’u 679, inda ya doke abokin takararsa David Vaughan wanda ya samu kuri’u 20.

Ogidi, wanda ya bayyana cewa akwai wakilai 775 na wucin gadi na zaben fidda-gwani, ya ce 709 ne aka amince da su a zaɓen.

A cewarsa, kuri’u 10 ne suka lalace a zaɓen.

Ogidi ya ce: “Jimillar wadanda aka amince da su yi zaben su 709 ne, kuma Olajide Adediran ya samu kuri’u 679, DAKOVA (David Kolawole Vaughan) ya samu kuri’u 20, kuma mun samu kuri’u 10 da su ka lalace.

“Bayan cika dukkan sharuɗɗan da ke cikin ka’idojin mu, ina so in sanar da Dr Olajide Adediran a matsayin ɗan takararmu, bayan ya samu kuri’u mafi rinjaye na 679. An bayyana shi a matsayin wanda ya lashe zaɓe.”

A jawabinsa na nasara, Adediran, wanda ya godewa ƴan takarar da su ka janye masa da kuma wadanda su ka fafata da shi a zaɓen, ya ce a shirye ya ke da ya ƙara da jam’iyar APC a babban zaɓe.

Ya yi alkawarin zama da dukkan masu neman tsayawa takara da shugabannin jam’iyyar domin yin amfani da iliminsu da gogewarsu a yunkurinsu na samun nasara a jihar Legas a jam’iyyar PDP.