Home Siyasa Abdullahi Adamu ya kama aiki a matsayin shugaban jami’yar APC na ƙasa

Abdullahi Adamu ya kama aiki a matsayin shugaban jami’yar APC na ƙasa

0
Abdullahi Adamu ya kama aiki a matsayin shugaban jami’yar APC na ƙasa

 

Sabon zaɓaɓɓen Shugaban Jam’iyar APC na Ƙasa, Abdullahi Adamu, da sauran ƴan Kwamitin Zartaswa na jam’iyar, NWC, sun kama aiki a yau Laraba, bayan an zaɓe su a Babban Taron jam’iyar a ranar 26 ga watan Maris.

Gwamnan Jihar Nassarawa da sauran kusoshin jam’iyar ne su ka raka Adamu ofishinsa a Shelkwatar APC a Abuja domin bikin kama aikin.

A tawogar kuma har da tsohon shugaban jami’yar na riko, Gwamnan Jihar Yobe, Mai Mala Buni.

Buni, yayin da ya ke danƙa wa Adamu ragamar aikin, ya shaida masa cewa akwai jan aiki a gaban jam’iyar yayin da a ke tunkarar zaɓen 2023.

A nashi jawabin, Adamu, wanda ya ke wakiltar Nassarawa ta Yamma a Majalisar Dattijai kafin zabar sa a matsayin shugaban jami’yar, ya ce zai haɗa kai da gwamnatin taraiya wajen kawo ƙarshen matsalar tsaro.

Da ya ke magana a kan harin jirgin ƙasa na ranar Litinin, Adamu ya ce gwamnati na maida hankali kan Aiyukan ta’addanci.

Daily Nigerian Hausa ta rawaito cewa Adamu shine gwamnan jihar Nassarawa da ga 1999 zuwa 2007.