
Daga Abba Ibrahim Gwale
Dan wasan kungiyar kwallon kafa ta Barcelona, Leonel Messi ya bayyana cewa abin bakin cikine dan wasa Neymar yakoma Barcelona ganin yadda dan wasan yabuga wasa a kungiyar ta Barcelona kuma ya lashe kofuna da dama a kungiyar.
Neymar yakoma PSG daga Barcelona a watan Agustan shekarar data gabata akan kuxi fam miliyan 200 wanda hakan yasa a yanzu xan wasan yafi kowanne xan wasa tsada a duniya kuma ya lashe kofin qasar Faransa.
Messi yace Neymar ya lashe manyan kofuna da suka haxa da gasar zakarun turai da gasar Laliga da kuma ragowar kofuna saboda haka har yanzu akwai Barcelona a zuciyarsa kuma idan yakoma Real Madrid zai kara musu karfi.
Messi yace yana bakin cikin ganin Real Madrid ta kara karfi saboda bayason ganin su suna lashe kofuna kuma idan har Neymar ya koma kungiyar zasu cigaba da cin kofuna da kafa tarihi kala-kala.
Sai dai yace bayason ganin sun lashe gasar zakarun turai da zasu fafata wasan karshe da Liverpool saboda bayason gani suna cin kofi.
Har ila yau Messi yace yana ganin kasarsa zata iya lashe kofin duniya ta za’a fara a kasar Rasha a wata mai kamawa inda yace shekaru hudu da suka wuce sunje wasan karshe yanzu kuma yana fatan zasu lashe kofin.
A karshe kuma ya bayyana cewa baya gasa da Ronaldo saboda kowa abinda yakeyi daban kuma suna kungiyoyin da basa shiri da juna saboda haka abinda yake gabansa kawai yakeyi.