Home Labarai ABIN TAUSAYI: Kwastoma ta yanke jiki ta fadi bayan ta zubar da Naira miliyan 2.3 a wata kasuwa a Abuja

ABIN TAUSAYI: Kwastoma ta yanke jiki ta fadi bayan ta zubar da Naira miliyan 2.3 a wata kasuwa a Abuja

0
ABIN TAUSAYI: Kwastoma ta yanke jiki ta fadi bayan ta zubar da Naira miliyan 2.3 a wata kasuwa a Abuja

Wata mata mai suna Rukayyat, ta yanke jiki ta fadi bayan da ta fuskanci cewa ta zubar da kuɗin ta naira miliyan 2.3 a kasuwar Abaji da ke Abuja.

Matar, kamar yadda Daily Trust ta rawaito, ta fadi ne a ranar Juma’a da misalin ƙarfe 9:45 bayan da ta je kasuwar saro kayan abinci.

Wani ganau, mai suna Yakubu Musa, wanda ya ce duk Juma’a matar na zuwa daga garin Auchi a jihar Edo, ya ce matar ta kira babu kudin nata ne bayan an kusan kammala auna mata hatsin da ta saya a buhuhuna.

A cewar sa, ta na duba kudin ta ga babu sai ya yanke jiki ta fadi ta na ta rusa ihu, inda ta rika fadin cewa kuɗin na bashi ne ta ciyo don ta yi kasuwanci.