
Uwar jam’iyyar PDP ta kasa ta yi watsi da rahotannin dake nuna cewar ‘Yan kungiyar Kwankwasiyya a jihar Kano sun yi zaben fidda gwani na wanda zai tsayawa jam’iyyar PDP takarar Gwamna a jihar.
Mai magana da yawun kakakin jam’iyyar PDP na kasa Uche Secondus wato Shehu Yusuf Kura ya shaidawa sashin Hausa na gidan Radiyo BBC cewar ba da Amincewar uwar jam’iyyar PDP ‘Yan Kwankwasiyya suka gudanar da zaben Gwamna ba.
Shehu Yusuf Kura ya Kara da cewar abinda ‘Yan Kwankwasiyya suka yi a Kano haramtacce ne kuma uwar jam’iyyar PDP ta kasa ba zata aminta da shi ba. A cewarsa za a sanya ranar zaben fidda gwani na Gwamnan Kano nan da kwanaki uku.
A Daren jiya ne dai ‘yan Kwankwasiyya suka ce sun gudanar da zaben fidda gwani na Gwamnan Kano inda suka zabi Surikin Kwankwaso Abba Kabiru Yusuf a matsayin dan takararsu.