Home Labarai Abuja: Kotu ta yanke wa wani mutum hukuncin sharar masallaci bisa laifin tara ɓarayi

Abuja: Kotu ta yanke wa wani mutum hukuncin sharar masallaci bisa laifin tara ɓarayi

0
Abuja: Kotu ta yanke wa wani mutum hukuncin sharar masallaci bisa laifin tara ɓarayi

A jiya Laraba ne wata kotun unguwar Dei-Dei da ke Abuja, ta umarci wani matashi dan shekara 28, Anas Ibrahim, da ya share masallacin Juma’a na unguwar na tsawon watanni shida bisa laifin tara ɓarayi.

Ibrahim, mazaunin kasuwar kayan marmari ta Zuba, Abuja, ya amsa laifinsa na zama da gungun ɓarayi, inda ya roƙi kotu da ta yi masa sassauci.

Alkalin kotun, Saminu Suleiman, ya umurci mai laifin da ya share babban masallacin Zuba na tsawon watanni shida ko kuma ya biya tarar Naira dubu 20.

Tun da fari, lauya mai shigar da kara, Chinedu Ogada, ya shaida wa kotun cewa an kama wanda ake tuhuma ne bisa bayanan sirri da aka samu daga wata majiya mai karfi da ta kai rahoton lamarin a ofishin ‘yan sanda na Zuba, Abuja, a ranar 2 ga watan Janairu.

Ogada ya ce majiyar ta yi ikirarin cewa wanda aka yanke wa hukuncin ya na tara ɓarayi ne kuma ya na sayar musu da miyagun kwayoyi, inda bayan sun sha sai su riƙa far wa mutanen da ba su ji ba ba su gani ba a Zuba.

Ogada ya ce a yayin binciken ƴansanda, wanda ake tuhuma ya amsa laifinsa amma duk kokarin da ake na cafke sauran ya ci tura.

Ya ce laifin ya ci karo da tanadin sashe na 30B na kundin dokar laifuffuka.