
Kamfanin Facebook sun bayarda bayanin cewar, ribar da suke samu ta karu a yayin da awannin da mutane suke sharewa suna mu’amala da shafukansu na facebook suka ragu matuka.
Facebook dai shi ne yake dauke da mutane masu yawa a cikin shafukan sada zumunta na duniyar intanet. Kamfanin Facebook dai ya bayyana cewar, yin tattaunawa mai amfani tsakanin abokai tafi muhimmanci sama da daukan dogon lokaci mutum yana kan facebook.
A sabida haka, kamfanin ya bayyana cewar ya gwammace ya karawa masu amfani da shi kwarin guiwa kan yin tattaunawa da musayan ra’ayi mai ma’ana sama da daukar dogon lokaci mai tsawo ana yin abinda ba shi da muhimmanci.
Wanda ya kirkiri shafin na Facebook, Mark Zuckerberg ya bayyana cewar suna aiwatar da wasu sauye sauye da zasu taimakawa masu amfani da shafin jin dadinsa, tare da taimaka musu wajen rage adadin lokacin da suke batawa akan facebook ba tare da yin wani abu mihimmi ba.
Sai dai kuma,mai lura da sashin gudanarwa na facebook din, yace samun miliyoyin masu amfani da facebook din suna shafe lokaci mai tsawo wajen amfani da shi yana taimakawa kamfanin bunkasa samun kudin shigarsa.
“Taimakawa mutane su sadu da abokansu don kulla zumunci, yafi mana muhimmanci sama da batun rage yawan adadin lokacin da mutum yake batawa yana amfani da facebook din”
“Zamu tabbatar mun inganta dukkan sadarwarmu da jama’a domin su samu gamsuwa a dukkan abubuwan da suke yi”
Ya kara da cewar, a ‘yan shekarun baya an dan samu matsaloli inda aka samu cunkoson sakwannin facebook da basa tafiya, amma daga baya aka gyara komai ya koma yana tafiya daidai.
Facebook na baiwa masu amfani da shi wani muhimmanci na daban, kuma kullum burinmsa shi ne samun gamsuwa da duk abinda mutum yake yi.
“Muna aiwatar da canje canje a ko da yaushe domin tabbatar da cewar muna tafiya da lokaci kuma da bukatun mutane” A cewar Zuckerberg.