
Bola Ahmed Tinubu, dan takarar shugabancin kasa na jam’iyyar APC, ya ce ba ya adawa da sake fasalin Naira da manufofin kudi na Babban Bankin Ƙasa, CBN, illa kawai ya na damuwa da halin da hakan ya jefa ƴan ƙasa.
Tinubu ya bayyana hakan ne a wata sanarwa da ya fitar a jiya Lahadi a Abuja, inda ya kara da cewa ya damu ne kawai da kawo cikas da aiwatar da manufar ta yi, tare da kuma wahalhalun da ya jawo wa al’ummar Najeriya baki daya.
Ya ce hakan ya faru ne musamman saboda a halin yanzu galibin ‘yan Najeriya ba za su iya cire kudaden su halak -malak su biya bukatun su ba.
Tsohon gwamnan jihar Legas ɗin ya lura cewa ‘yan makonnin da suka gabata sun kasance kalubale ga ‘yan Najeriya, musamman masu kanana da matsakaitan sana’o’i, SMEs.
Ya kara da cewa, wadanda ke fuskantar kalubalen su ne talakawa da marasa galihu da kuma wadanda rayuwarsu ta dogara da hada-hadar kudi ta yau da kullum.