
Cibiyar Dimokuradiyya da Ci Gaba, CDD, ta bayyana cewa yankin Arewa-maso-Yamma na kasar nan na ɗauke da ƴan ta’adda, waɗanda a ka fi sani da ƴan fashin daji sama da suke addabar yankin baki ɗaya.
A cikin rahotonta na watan Fabrairu mai taken ‘Matsalar ‘Yan fashin daji a Arewa-maso-Yamma: Bayanai kan abubuwan da su ke haddasa rikici’, CDD ta ce waɗannan ‘yan ta’addan ne ke da alhakin kashe mutane sama da 12,000 da kuma tarwatsa sama da gidaje miliyan guda a yankin.
Rahoton ya ƙara da cewa ta’addancin ya kuma tilastawa yara sama da miliyan 1 barin zuwa makaranta a jihohin Zamfara da Sokoto da Kebbi da Katsina da kuma Kaduna.
Kungiyar ta masu rajin kare dimokradiyya , a cikin rahoton mai shafuka 42 da Daraktarta ta yammacin Afirka, Idayat Hassan ta sanya wa hannu, ta koka da cewa kashe-kashen da ake yi a yankin Arewa-maso-Yamma ya watsu zuwa jihar Neja da kuma wasu jihohin yankin Arewa ta tsakiya.
A cewar rahoton, tashe-tashen hankulan ya koma ga cikakken yaƙi da ƴan ta’adda, inda su ke fitowa fili su fafata da kuma kai hari kan cibiyoyin tsaro da cibiyoyin gwamnati.