
Wasu ƴan ta’adda a daren ranar Litinin, sun kashe Salisu Idris, Mai-garin Nyalun na Ƙaramar Hukumar Wase a jihar Plateau.
Jaridar Saily Trust ta rawaito cewa ƴan bindigar da ake zargin sun kuma bindige wasu mazauna unguwar biyu.
Kakakin Rundunar ƴan sandan Jihar, DSP Alabo Alfred, a lokacin da yake tabbatar da faruwar lamarin, ya ce mutane uku ne suka mutu a harin, inda ya ƙara da cewa har yanzu babu cikakken bayani.
Wadanda abin ya shafa, a cewar mazauna kauyen, an kashe su ne a kauyen lokacin da ‘yan bindigar suka isa unguwar a kan babura suka fara harbe-harbe.
Mazauna yankin sun shaida wa wakilin Daily Trust cewa maharan da suka kai farmaki kauyen da misalin karfe 8:00 na dare, sun kuma yi awon gaba da wasu mutane biyar daga cikin mutanen da suka hada da matan aure biyu.
Shapi’i Sambo, shugaban matasa a Wase ya shaida wa jaridar cewa ƴan bindigar sun kuma yi awon-gaba da babura da dama.
Shugaban matasan ya ce “Maharan sun zo ne da yawa kuma suka fara harbe-harbe kai tsaye. Kai tsaye gidan sarkin gargajiya suka je, suka kashe shi suka yi awon gaba da mutum biyar na iyalansa. Haka kuma sun kashe wasu mutane biyu lokacin su na shirin tsere wa.”