
A yau Lahadi ne gwamnatin Jihar Kaduna ta tabbatar da cewa wasu ƴan bindiga sun kai hari kan masu ibada a wata coci, inda suka kashe mutane uku tare da raunata wasu biyu a Ƙaramar Hukumar Kajuru da ke jihar.
Kwamishinan tsaro na da harkokin cikin gida, Samuel Aruwan ya tabbatar da faruwar lamarin a wata sanarwa da ya fitar a Kaduna.
Aruwan ya ce, “A wani yanayi na takaici, jami’an tsaro sun kai rahoto ga gwamnatin jihar Kaduna cewa ƴan bindiga sun kai hari a Ungwan Fada, Ungwan Turawa da Ungwan Makama a yankin Rubu na karamar hukumar Kajuru.”
A cewar rahoton, ƴan fashin sun far wa ƙauyukan ne a kan babura, inda suka fara daga Ungwan Fada, sannan suka shiga Ungwan Turawa, kafin daga bisani Ungwan Makama da Rubu.
Ya bayyana cewa, a ƙauyen Rubu, ƴan bindigar sun kai hari a cocin Maranatha Baptist da Cocin St. Moses Catholic Church.
“An tabbatar da mutuwar mutane uku a hare-haren, kuma mutane biyu sun ji rauni – ɗaya daga cikinsu namiji ne da mace daya da ba a tantance ko wacece ba.
“An kuma yi garkuwa da wasu mutanen yankin da ba a tantance adadinsu ba,” a cewar rahotanni.
“‘Yan fashin sun yi awon gaba da shaguna tare da kwashe wasu kayayyaki daga kauyukan,” in ji shi.
Aruwan ya ce, mukaddashiyar gwamnan jihar, Hadiza Balarabe, ta bayyana matukar alhini a kan harin sannan ta yi Allah wadai da harin da kakkausar murya.
Ta mika sakon ta’aziyyarta ga iyalan wadanda aka kashe, yayin da ta yi addu’ar Allah ya jikan su.