
Wasu ‘yan ta’adda sun kashe tsohon kwamishinan Hukumar Ƙidaya ta Ƙasa, NPC, Zakari Umaru Kigbu a jihar Nasarawa, tare da yin garkuwa da ‘ya’yansa mata biyu.
Jaridar Daily Trust ta tattaro cewa lamarin ya faru ne da sanyin safiyar Lahadi a gidan Kigbu ɗin da ke Azuba Bashayi ‘, a Ƙaramar Hukumar Lafiya ta jihar Nasarawa.
An jiyo cewa masu garkuwa da mutanen sun kuma bukaci a biya su Naira miliyan 50 domin a sako ƴaƴan nasa mata su biyu.
Wani dan uwan marigayin da bai so a bayyana sunansa ya tabbatar da faruwar lamarin a safiyar Lahadi a Lafiya, babban birnin jihar Nasarawa.
Ya ce, “Malam. Wasu ‘yan bindiga sun kashe Umaru-Kigbu a daren jiya a gidansa da ke Azuba Bashayi, karamar hukumar Lafiya ta Jihar Nasarawa, sannan kuma an yi garkuwa da wasu ‘ya’yansa mata guda biyu.”
Marigayin, mai shekaru 60, jami’in sojan sama ne mai ritaya.
An tattaro cewa, har zuwa lokacin da aka kashe shi, malami ne a sashen yada labarai na sadarwa, lsa Mustapha Agwai Polytechnic, Lafia (IMAP), kuma tsohon kwamishinan tarayya na NPC, mai kula da jihar Nasarawa.