Home Labarai Ƴan ta’adda sun samo sabuwar hanyar sadarwa duk da an katse layukan wayar salula- Gwamnatin Katsina

Ƴan ta’adda sun samo sabuwar hanyar sadarwa duk da an katse layukan wayar salula- Gwamnatin Katsina

0
Ƴan ta’adda sun samo sabuwar hanyar sadarwa duk da an katse layukan wayar salula- Gwamnatin Katsina

 

Gwamnatin Jihar Katsina ta baiyana cewa yanzu ƴan ta’adda a jihar da wayar salula ta oba-oba, wacce a ka fi sani da walkie talkie su ke amfani.

Sakataren Gwamnatin jihar, Mustapha Inuwa ne ya baiyana hakan a taron manema labarai da ya gudanar a Katsina a yau Alhamis.

Inuwa ya nuna rashin jin daɗin yadda ƴan ta’addan ke ƙirƙiro da sabbin dabaru na ci gaba da kai hare-hare a kan al’umma.

Ya ƙara da cewa duk wasu hanyoyi na dabaru da jami’an tsaro ke amfani da su wajen daƙile aiyukan ƴan ta’addan, amma sai sun yi ƙoƙarin ɓullo da na su dabarun.

“Haka su ke kaiwa masu babura hari domin su yi amfani da man fetur ɗinsu. Su kaiwa masu motoci hari domin amfani da man fetur ɗinsu. Duk dai wasu hanyoyi na daƙile aiyukansu sai sun yi amfani sun ɓullo da nasu.

“Abin da ya fi damun mu ma shine yadda yanzu ƴan ta’addan ke amfani da wayar salula ɗin nan mai amfani da zangon rediyo wato oba-oba ko walkie talkie. Amma duk da haka ana samun nasara a kansu,”in ji shi.

Inuwa, wanda shi ne shugaban kwamitin tsaro na jihar ya ƙara da cewa gwamnatin jihar ba za ta gajiya ba har sai ta shawo kan lamarin.

Ya kuma yi kira da mutane da su ƙara haƙuri domin cewa matakan tsaro da a ke ɗauka, duk da cewa a kwai takura a ciki, amma an yi ne don amfanin al’umma ba wai don a muzguna musu ba.

A tuna cewa a watan Satumba ne gwamnatin jihar ta katse layukan wayar sadarwa a wani mataki na daƙile aiyukan ƴan ta’addan a wasu ƙananan hukumomi 13.