Home Labarai Ƴan ta’adda sun yi wa sojoji kwanton-ɓauna, inda su ka kashe 2 da raunata 4 a Katsina

Ƴan ta’adda sun yi wa sojoji kwanton-ɓauna, inda su ka kashe 2 da raunata 4 a Katsina

0
Ƴan ta’adda sun yi wa sojoji kwanton-ɓauna, inda su ka kashe 2 da raunata 4 a Katsina

 

 

Wasu ƴan ta’adda sun yi wa motar sojoji mai sulke kwanton-ɓauna, inda su ka kashe sojoji biyu tare da raunata wasu hudu a yankin Shimfida da ke Ƙaramar Hukumar Jibiya ta jihar Katsina.

Wata majiya mai inganci ta shaida wa jaridar Thisday ta wayar tarho cewa an yi wa sojojin kwanton-ɓaunar ne a kan hanyar Shimfida zuwa Gurbi da misalin karfe 10 na safe yayin da suke raka al’ummar garin zuwa garin Jibiya domin siyan kayan abinci.

A cewar majiyar, sojojin da aka kashe na daga cikin dakarun bataliya ta 32 na sojojin Najeriya da aka girke a garin Shimfida mai fama da rikici.

Majiyar ta bayyana cewa, motar ta sojojin da ke rakiyar mazauna garin ta taka bama-bamai da ƴan ta’addan suka dasa a kan titin a kan hanyar Shimfida-Gurbi maras motsi.

Ya kara da cewa sojojin biyu sun mutu nan take, yayin da wasu hudu suka samu raunuka daban-daban a lokacin da bam din ya tashi.

Sannan kuma alwani Laftanar Musa, shugaban tawagar ba a ganshi ba bayan faruwar lamarin.