
A daren yau Litinin ɗin nan ne dai wasu da a ke zargi ƴan ta’adda ne su ka tashi bam a kan layin dogo na jirgin ƙasan Abuja-Kaduna, inda su ka samu nasarar tsayar da jirgin cak.
Wasu sahihan majiyoyi ne su ka tabbatar da harin ga jaridar DAILY NIGERIAN a daren nan na Litinin, inda su ka ce harin ya faru ne a wani waje tsakanin Katari da Rijana.
Ɗaya da ga cikin fasinjojin ya tabbatar da harin ya wayar salula ya ce maharan sun kewaye jirgin su na ta harbin shi.
“Duk fasinjojin na kwance a kasa a cikin jirgin a halin da ake ciki yanzu. Ƴan ta’addan ne ke ta harbin kan me uwa da wabi. Mun cikin bala’i,” in ji wani fasinja da ya ke cikin firgici.
Wasu majiyoyi da ga ma’aikatar jirgin ƙasa sun tabbatar da cewa Dawaki fasinjoji 970 a cikin jirgin.