
Hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa ta nesanta kanta daga wani adireshin yanar-gizo cewa ta na ɗaukar ma’aikata, wanda ke yawo a shafukan sada zumunta da sauran kafafe.
INEC, a wani sako da ta wallafa a shafinta na Twitter da yammacin jiya Talata, ta bayyana adireshin yanar gizo: ‘inecnigeria.govservice.site’ a matsayin na bogi, tana mai cewa sahihin adireshinta shi ne; ‘pres.inecnigeria.org da kuma inecpress-app.com/pres.’
“An ja hankalinmu kan wani sako na daukar ma’aikata na bogi da ake yadawa a kafafen sada zumunta daban-daban, da shafukan yanar gizo da ake yawan ziyarta da nufin damfarar ‘yan kasa da ba su ji ba ba su gani ba.
“Mu na kira ga ƴan ƙasa da su yi watsi da wannan adirwshi na yanar gizo na ƙarya kuma su guji faɗa wa hannun ƴan damfara,” inji INEC.
Har ila yau, INEC ta ce ta lura cewa aikin daukar ma’aikata na wucin-gadi kyauta ne, yana mai cewa, “Ba a buƙatar biyan kowane nau’in kuɗi a duk lokacin aikin.