
A wani yanayi na al’ajabi, inda ba kasafai a ka fiye gani ba, wani alƙalin wasa ya busa tashi sau biyu a wasa ɗaya kafin mintuna 90 na ka’ida.
Alƙalin wasa, Janny Sikazwe, shine ya yi wannan aika-aika, a ci gaba da wasannin gasar cin kofin ƙwallon ƙafa na nahiyar Afirka na shekarar 2021, AFCON 2021.
A jiya ne alƙalin wasa Sikazwe ya jagoranci wasan Mali da Tunisia, inda Mali ta doke Tunisia 1-0.
Sai dai kuma a na tsaka da wasan ne, a daidai minti na 85, kawai sai Sikazwe, ɗan ƙasar Zambia, ya busa tashi, lamarin da ya haifar da cece-kuce da ga ƴan wasa da kociyoyin ƙasashen biyu.
Bayan an ankarar da alƙalin wasan ne, sai a ka dawo domin a karashe sauran mintuna 5 ɗin wasan, kamar yadda doka ta tanada.
Ana dawowa, an take wasa a na yi, daidai minti na 89, da daƙiƙa 43, sai Sikazwe ya ƙara busa tashi, kafin dai a kai minti 90 na ƙa’idar wasan ƙwallon ƙafa.
Bayan nan ne sai tawogar Tunisia, wacce da ma an jefa mata ƙwallo a raga, ta ci gaba da ƙorafi ga alƙalin wasan.
Kawo yanzu dai ba a sani ba ko hukumar ƙwallon ƙafa ta Afirka za ta ɗauki mataki a kan alƙalin wasan.