
Wani kwamiti na ma’aikatar ilimi mai zurfi ta Afganistan ya ce yana kan shirin sake bude jami’o’i ga dalibai mata, kamar yadda kafafen yada labarai na kasar suka ruwaito a yau Litinin.
Kwamitin ya bayyana hakan ne a lokacin wani rahoto na shekara-shekara na ma’aikatar.
“Za mu raba shi ga jama’a idan an kammala shirin,” in ji rahoton.
Mukaddashin ministan ilimi mai zurfi, Lutfullah Khairkhwa ya ce har yanzu ba a bayyana lokacin kammala shirin ba.
Ya zuwa yanzu dai an hana mata shiga jami’o’i a kasar Afganistan.
Ma’aikatar Ilimi mai zurfi ta sanar da hana ilimin mata a watan Disambar 2022.