Home Kasuwanci Ƴan Afirka da dama ba sa iya sayen biredi — AfDB

Ƴan Afirka da dama ba sa iya sayen biredi — AfDB

0
Ƴan Afirka da dama ba sa iya sayen biredi — AfDB

 

 

Bankin Raya Ƙasashen Afirka, AfDB, ya ce a halin yanzu farashin biredi ya wuce yadda gidaje da dama a nahiyar Afirka ke iya saya, sakamakon karin farashin abinci da rikicin Russia da Ukraine ya haddasa.

Shugaban bankin, Dakta Akinwumi Adesina ne ya bayyana hakan a wani jawabi da ya fitar a shafinsa na Twitter na AfDB a yau Alhamis.

Adesina ya gabatar da jawabin ne a Kwamitin Kudi na Majalisar Dattawan Amurka kan ayyukan Jihohi da na kasashen waje mai taken: “Tsaron Abinci na Duniya da Rikicin COVID-19: Martanin Amurka da Zaɓaɓɓun Manufofi’’.

Ya ce Ukraine na fitar da kashi 40 na alkama da masara zuwa Afirka.

Adesina ya ambato Majalisar Dinkin Duniya na cewa “kasashen Afirka 15 sun shigo da fiye da rabin alkama, da yawancin taki da mai daga Ukraine da Russia”.

Adesina ya ce nahiyar na kuma fuskantar matsalar asarar alkama da masara da yawansu ya kai tan miliyan 30 da ba za su iya zuwa daga Russia ba yayin da rikicin ya ɓarke.

A cewarsa, taɓarɓarewar tattalin arziki daga yakin Russia a Ukraine ya sa dukkanmu za mu biya karin kudi don sanya abinci a kan teburan mu.