
Wani ma’aikacin gwamnati, Ibe Kufu ya roki wata kotun gargajiya da ke Jikwoyi a Abuja da ta raba aurensa da mai ɗakin sa sabo da ta ɓarnatar da Naira miliyan 2 da ya bata ta ja jari.
Kufu ya baiyana haka ne a wata takardar korafi da ya kai kotun.
“Mata ta almubazzara ce. Ta kasa yi min bayanin Naira miliyan biyun da na bata ta ja jari,” in ji shi.
Ya kuma shida wa kotun cewa mai ɗakin nasa na ƙoƙarin hallaka shi, inda ya ce ta faɗa masa za ta kashe shi a lokuta da dama.
Ya kuma shaida wa kotun cewa matar ta sa na janyo saurayinta gidansa a duk lokacin da ya yi tafiya.
Saboda haka ne mai ƙarar ya roƙi kotun da ta raba auren ta kuma bashi ƴaƴansa.
Sai dai kuma matar ta sa, Omar, wacce yar kasuwa ce, ba ta je kotun ba.
Alƙalin kotun, Labaran Gusau, ya ɗage ƙarar sai ranar 24 ga watan Maris domin sauraron ƙarar.