Home Labarai Ma’aikatan ƙidaya na wucin-gadi sun yi zanga-zangar ƙin biyan su haƙƙoƙinsu a Bauchi

Ma’aikatan ƙidaya na wucin-gadi sun yi zanga-zangar ƙin biyan su haƙƙoƙinsu a Bauchi

0
Ma’aikatan ƙidaya na wucin-gadi sun yi zanga-zangar ƙin biyan su haƙƙoƙinsu a Bauchi

Kimanin ma’aikatan wucin-gadi 467 na hukumar kidaya ta kasa, NPC ne a jihar Bauchi su ka fito kan tituna domin nuna rashin amincewarsu da kin biyansu haƙƙunansu.

An gudanar da zanga-zangar ne a titin Wunti da ke cikin birnin Bauchi a jiya Talata.

Ma’aikatan na wucin-gadi sun riƙa daga kwalaye da rubuce-rubuce kamar su “Babu albashi, ba aiki,” da “Muna neman alawus din mu daga ofishin NPC”.

Kakakin ma’aikatan wucin-gadin, Abbas Adamu, a lokacin da ya ke jawabi ga Daraktan NPC da ma’aikatan jihar a Bauchi, ya ce: “Mun yi aikinmu amma har yanzu ba mu samu alawus dinmu ba.

“A madadin ma’aikatan kidaya na wucin-gadi na NPC 2023, wadanda su ka shiga a matsayin jami’ai na musamman da masu gudanarwa don aikin kidayar 2023 mai zuwa.

“Mun zo nan ne don sanar da Hukumar cewa mu a cikin jerin sunayen da aka makala ba mu karbi alawus din horon da aka yi mana a Abubakar Tatari Ali Polytechnic da Jami’ar Abubakar Tafawa Balewa, Bauchi ba daga ranar 23 ga watan Janairu zuwa 5 ga watan Fabrairu na aiki na musamman da masu gudanarwa bi da bi,” inji shi.

Da ya ke mayar da martani, Hudu Baballe, Daraktan NPC na jihar, ya yaba wa ma’aikatan wucin-gadin bisa gudanar da zanga-zangar cikin lumana ba tare da tashin hankali ba.

Baballe ya umarci ma’aikatanda suka ji ransunya ɓaci da su kwantar da hankalinsu domin hukumar za ta yi duk mai yiwuwa don duba halin da suke ciki.