Home Labarai Ma’aikatan jirgin ƙasan Nijeriya sun fara yajin aiki

Ma’aikatan jirgin ƙasan Nijeriya sun fara yajin aiki

0
Ma’aikatan jirgin ƙasan Nijeriya sun fara yajin aiki

 

An rufe tashoshin jirgin ƙasa a fadin Najeriya bayan ma’aikatan Hukumar Sufurin Jiragen Ƙasa sun fara yajin aiki.

Jaridar Aminiya ta rawaito cewa tun a cikin dare kafin wayewar garin Alhamis ne ma’aikatan su ka rufe tashoshin jiragen ƙasan domin fara yajin aikin da suka shirya na kwanaki uku.

Ma’aikatan sun tsunduma yajin aikin gargaɗi ne domin neman a yi musu ƙarin albashi da kuma inganta yanayin aikinsu.

A ranar Asabar, Ministan Sufurin Jiragen Kasa, Rotimi Amaechi, ya yi wata tattaunawa da shugaban kwadago daga cikin ma’aikatan, domin shawo kan matsalar, amma aka tashi ba tare da cim ma daidaito ba.

Daga baya ministan ya sake kiran wani zama da su, nan ma haƙa ba ta cim ma ruwa ba.