
Ma’aikatan kula da muhalli na Abuja sun yi barazanar rufe maƙabartu da babbar cibiyar jibge bahaya ta birnin, matuƙar hukumomi suka gaza cika alƙawarin fara biyansu da sabon tsarin albashi.
BBC Hausa ta rawaito cewa ma’aikatan sun yi barazanar ne bayan ƙungiyarsu ta cimma yarjejeniya da hukumomin Abuja sakamakon yajin aikin gargaɗi da ya kai ga rufe maƙabartar Gudu, kafin buɗe ta daga bisani.
Hukumar kare Muhalli ta Abuja ta ce ana ci gaba da tantance bayanai don ganin an fara biyan ma’aikatan sabon tsarin albashin da aka amince da shi tun a 2019.
Ma’aikatan kula da muhallin na Abuja sun ce za su rufe maƙabartar Gudu da ta Gwarinpa da ofisoshin kare muhalli da tashoshin aikin shara da babbar cibiyar jibgewa da tace bahaya ta Wupa a ƙarshen watan Satumba matuƙar hukumomi suka gaza fara biyansu da sabon tsarin albashi.
Maƙabartun Gudu da na Gwarinpa da ke ƙarƙashin Hukumar kare muhalli ta Abuja, na da matuƙar muhimmanci ga birnin Abuja don kuwa a nan ne ake bizne gawawwakin da ba a san masu su ba.
Na mutanen da suka rasu ta kamar sanadin hatsari da waɗanda aka tsinta, da gawawwakin da makusanta ba su je sun karɓa a asibitoci ba.
Shugaban ƙungiyar ma’aikatan, Mukhtar Bala, ya ce kiraye-kirayen al’umma ne ya sanya su buɗe maƙabartar ta Gudu kafin kawo ƙarshen yajin aikin gargaɗi da suka yi a ranar Alhamis.
Shugaban ƙungiyar ma’aikatan Kwamared Mukhtar Bala ya ce ma’aikatan kula da muhalli na Abuja sun ƙunshi jami’an duba-gari da Jami’an tsaftace birni da ma’aikatan kula da bututan kwashe bahayar Abuja waɗanda suka haɗar da na babbar tashar tace bahaya ta Wupa da jami’an bin diddikin tsarin gine-gine da lauyoyin hukumar da sauransu.
A cewarsa, a shekara ta 2019 ne, ministan Abuja ya amince a fara biyansu sabon tsarin albashin, amma har yanzu ba su ga komai a ƙasa ba.
Injiniya Osilama Braimah, wanda darakta ne a hukumar kare muhalli ta Abuja ya yi wa BBC karin bayani kan wannan lamari inda ya ce gwamnati ta amince a soma biyan ma’aikatan sabon tsarin albashin nasu.
Haka kuma ya ce sakamakon alkawarin da minista ya yi musu na cewa zuwa watan Satumba za a soma biyansu, sai a dakata a gani.
A baya-bayan nan dai Najeriya dai na fama jerin yajin aikin ma’aikata a fannoni da dama kama daga malaman jami’o’i da ma’aikatan lantarki da masu gidajen burodi, yayin da ƙasar ke faɗi-tashi sakamakon matsin tattalin arziƙi da hauhawar farashin kayayyaki da suka addabi duniya.