
Ma’aikatan sufuri a Lebanon, a yau Alhamis sun rufe dukkanin manyan tituna da hanyoyin sufuri a Beirut, babban birnin ƙasar, inda su ke zanga-zangar ƙarin farashin gas ɗin girki, abinci da kuma karyewar darajar kuɗin ƙasar.
Ƙungiyar ma’aikatan sufurin ƙasa ce ta kira zanga-zangar.
Wani ɗan ƙungiyar, Ahmad Qubaisi da ga Nabatieh ya ce “dole ne mu ɗauki wannan matakin. A baya mun yi irin wannan matakin na kariya, inda mu ka toshe tituna tun da ga karfe 5 na safe har zuwa 10 ma safe, sannan da ga karfe 3 na yamma zuwa karfe 8 na yamma.
“Yau ma ga mu mun fito tun karfe 4 na safe. Mu bukatun mu a kan canjin kudin Amurka ne da kuma sauƙaƙa farashin kayan abinci.
“Farashin fetur ya ki daidaito kuma na ci gaba da tashin gwauron zabi har ma a wannan lokacin da mu ke zanga-zanga,”