
Wasu ma’aikatan wucin-gadi na Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa, INEC, a Jihar Neja, sun yi barazanar kauracewa zaben Gwamnan Jihar da za a yi a ranar 11 ga Maris, bisa zargin rashin biyansu alawus-alawus.
Ma’aikatan wucin-gadin da su ka zanta da manema labarai sun ce ba a biya su alawus-alawus na horo da na zabe na zaben shugaban kasa da na ‘yan majalisun tarayya da suka gudanar a ranar 25 ga watan Fabrairu ba.
Cikin nuna takaici, ma’aikatan sun yi ƙorafin cewa duk da tsananin damuwa da barazana ga rayuwarsu, har yanzu ba a biya su cikakken alawus-alawus din su ba.
Jaridar DAILY NIGERIAN ta ruwaito cewa, akwai fargabar cewa karancin naira da ake fama da shi a kasar nan zai shafi biyan ma’aikatan da ke yi wa hukumar aiki.
Ko a ranar 24 ga watan Fabrairu, shugaban INEC, Mahmood Yakubu, ya bayyana cewa babban bankin Najeriya, CBN, ya bayar da tsabar kudaden da hukumar ta buƙata domin gudanar da zaben cikin sauki.