Home Kasuwanci Ma’aikatan wutar lantarki na barazanar sake rufe cibiyar rarraba wuta ta kasa

Ma’aikatan wutar lantarki na barazanar sake rufe cibiyar rarraba wuta ta kasa

0
Ma’aikatan wutar lantarki na barazanar sake rufe cibiyar rarraba wuta ta kasa

 

Akwai fargaba a kasar nan yayin da ma’aikatan wutar lantarki, karkashin inuwar kungiyar ma’aikatan wutar lantarki ta kasa, NUEE, su ka sake yin barazanar rufe cibiyar rarraba wutar lantarki ta kasa.

A cewar ma’aikatan wutar lantarkin, wa’adin makwanni biyu da gwamnatin tarayya ta yi na sasanta wa kan rikicinsu ya wuce kuma ba a yi komai ba

Da ya ke zantawa da manema labarai a Kaduna a jiya Alhamis, Comrade Dukat Ayuba, sakataren kungiyar na shiyyar Arewa maso Yamma na NUEE, ya bayyana cewa yayin da ake ci gaba da tattaunawa, za a rufe cibiyar rarraba wutar lantarki ta kasa.

A cewarsa, batun jinginsr da ɓangaren wutar lantarki ga ƴan kasuwa duk harkar cuwa-cuwa ce, inda ya bayyana cewa bayan shekaru tara babu wani abin da ya canza wajen inganta samar da wuta, musamman ga masu amfani da wutar lantarki.

Ya kara da cewa, “Don haka ne muka yi yaki da mayar da bangaren wuta ga ƴan kasuwa saboda masu zuba jari ba su da kwarewa a harkar.”

” A matsayinmu na ‘yan Najeriya, mun shawarci gwamnati da kada ta yi hakan. Amma gwamnati ta dage kan yin hakan,” in ji shi