
Abu ne sananne cewa fafutuka da kujuba-kujuba ta lamarin shugabanci ga ƴan siyasa, musamman shugabannin ƙananan hukumomi, waɗanda suka fi kusanci da jama’a, har takan kai wasun su na wasan ɓuya da talakawansu, musamman na yawan buƙatu gami da halin da lamarin tallttalin arzikin kasa.
A yanayin mulkin yanzu ma, shugabannin ƙananan hukumomi na ƙaurace wa ofisoshinsu, inda yawanci su ke bin gwamnoni wasu guraren taruka na siyasa da kuma kusan tare wa a Abuja domin ƙule-ƙulle a kan ci gaban siyasar su.
Hakazalika, duk wani ɗan siyasa, musamman idan ya kai matsayin Shugaban Ƙaramar Hukuma, to yawanci ya yi sallama da duk wata sana’ar hannu da ya taso ya na yi tun yarinta, inda wasu ma tun kan su samu muƙami, ko kuma sun samu muƙamin da bai kai na shugaban ƙaramar hukumar ba, za su ajiye wannan sana’a ta su, su kuma rungumi siyasar.
Sai dai kuma a an Ƙaramar Hukumar Birnirwa da ke Jihar Jigawa labarin ba haka yake ba, domin kuwa
duk da matsayin da Allah ya ba shi na shugabantar ƙaramar hukumar, Umar Baffa bai bar sana’ar shi ta ɗinki, wacce ya koya ya kuma buɗe ido da ita tun tale-tale ba.
Duk da cewa Baffa, shine zaɓaɓɓen Shugaba mai iko a Ƙaramar Hukumar ta Birniwa, ganin cewa yana da dogara wa a ƙasan sa, kamar kansiloli da sauran jami’ai a karkashinsa, hakan bai hana shi ya koma shafinsa na ɗinki ya hau keke ya ci gaba da dinka kayan kwastomomin sa ba.
Ya shaidawa wakilin DAILY NIGERIAN HAUSA da ya ziyarce shi a shagon dinkin nasa a yau Alhamis cewa wannan sana’a ce da ya koye ta ne tun ya na matakin karatu na firamare, kuma ya rike ta hannu biyu-biyu, inda a sanadiyar ta ne yakai duk matakin da yakai yanzu haka.
Ko da a ka tambayeshi wajen lamarin tafiyar da shugabancin na karamar hukumar, sai Baffa ya kada baki ya ce, babu shakka ba shi da wata mishkila wajen tafiyar da shugabancin na Karamar Hukumar.
Ya ce a cikin kasa da shekara daya da zama shugaban karamar hukumar, ya samar da ayyukan raya kasa daban daban waɗanda su ka haɗa da sha’anin Ilimi, lafiya tallafawa mata da matasa da kuma inganta tsaro.
Ya kuma gode wa Gwamnan Jihar Jigawa, Badaru Abubakar bisa manyan ayyukan alheri da ya ke samar masu a yankin nasu.
Baffa ya kuma shawarci sauran shuwagabanni masu rike da madafun iko da su yi kokari wajen sauke nauyin da ya rataya a wuyansu.
Kazalika ya yi kira ga matasa da su himmatu wajen rike sana’oin hannu wanda za su taimaki kansu dama sauran al’umma baki daya don samun dogaro da Kai.