
Ma’ajin jam’iyyar PDP na shiyyar Arewa-maso-Gabas, Galadima Abbas Itas, ya fice daga jam’iyyar, biyo bayan abin da ya bayyana a matsayin “rashin adalci ” da da aka yi wa ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar kuma gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike.
Tun da fari, kwamitin da a ka kafa ya fitar da mataimakin ɗan takarar shugaban ƙasa ga Atiku Abubakar, ya zaɓi Wike a matsayin abokin takarar.
Sai dai a wani yanayi na daban, Atiku ya bayyana gwamnan jihar Delta, Ifeanyi Okowa a matsayin mataimakinsa, matakin da da yawa daga cikin masu biyayya ga Wike suka bayyana a matsayin “cin amana.”
A cikin takardar murabus ɗin, mai ɗauke da kwanan watan 12 ga watan Yuli kuma aka aika wa shugaban gundumar Ƙaramar Hukumar Itas Gadau ta jihar Bauchi, Galadima ya ce zaben Okowa ya saɓa wa ƙa’idarsa ta siyasa da akidarsa.
A cewarsa, halin da jam’iyyar ke ciki a halin yanzu ba zai sa a amince da cewa jam’iyyar ta adawa a shirye take ta ƙwaci mulki a 2023 ba.
Ya ce: “Ban rubuta takardar murabus ɗin nan nawa ba sai da na tuntuɓi ɗumbin magoya bayana, abokan siyasa. Hakan kuma wani mataki ne na mayar da martani ga rashin adalci da ake yi wa Mai Girma Gwamna, Barr Ezenwo Nyesom Wike, CON, Gwamnan Jihar Ribas.
“Hakazalika, zaben mai girma Ifeanyi Okowa a matsayin abokin takarar shugaban kasa ya saɓa wa ka’idar siyasa da akida na, don haka ya kara karfafa shawarar murabus ɗina.
“A matsayina na mai ruwa da tsaki, rashin adalci da aka yiwa mambobin kungiyar da aka kafa ya yi babbar barazana ga muradun siyasar shugabanninmu da mu, wanda hakan ya sa na yi murabus don nuna rashin amincewa da yadda abubuwa ke faruwa a jam’iyyar,” in ji Mista Itas.