Home Labarai Kuɗaɗen da aka sace a shekaru 8 sun isa a rabawa ko wanne ɗan Nijeriya N732,000 — Naja

Kuɗaɗen da aka sace a shekaru 8 sun isa a rabawa ko wanne ɗan Nijeriya N732,000 — Naja

0
Kuɗaɗen da aka sace a shekaru 8 sun isa a rabawa ko wanne ɗan Nijeriya N732,000 — Naja

Kwamishiniya a Hukumar kula da Harkokin Ƴan sanda ta Ƙasa, PSC, Najatu Mohammed, ta bayyana cewa kudaden da masu rike da mukaman gwamnati suka wawashe a cikin shekaru 8 da suka gabata sun isa a raba wa kowane dan kasa Naira dubu 732.

Ta bayyana hakan ne a wata tattaunawa ta musamman da Freedom FM Kano, a wani bangare na bikin bayar da lambar yabo da lacca da aka gudanar kwanan nan don karrama wani jami’in dan sanda, Daniel Itse Amah.

Cibiyar Wayar da kan Al’umma kan Adalci da Amana, CAJA, ce ta shirya taron, tare da hadin gwiwar Cibiyar Penlight.

A cewar Najatu, idan har ba a shawo kan lamarin cin hanci ƙasar nan ba, nan da 2030 kowane dan kasa zai iya samun sama da Naira miliyan 1.4 idan za a dawo da kudaden da aka wawashe a raba.

Ta ce hanya daya tilo da kasar za ta iya gyara wannan ta’ada ita ce ta nuna wa jami’an gwamnati masu sa wawashe dukiyar talakawa kuskuren su da kuma kin zabar su.