
Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa, INEC ta ce akwai sama da katikan zaɓe dubu ɗari uku da tamanin da tara da masu su ba su je sun karɓa ba a jihar Kano.
Kwamishinan zaɓe na jihar, Riskuwa Shehu ne ha bayyana haka lokacin da Kwamishinan Tarayya na Hukumar Ƙorafe-ƙorafe, Ahmad Daɗinkowa ya kai masa ziyara a jiya Alhamis.
Riskuwa, wanda ya samu wakilcin Sakataren Gudanarwa, Garba Lawan ya ce katikan da ba a karɓa ɗin be tun na shekarun 2011 zuwa 2018 ne.
Ya ce mutane ba sa son zuwa su karɓi katin zaɓen su.
Ya yi kira ga masu ruwa da tsaki da su zaɓe dantse wajen wayar da kan al’umma don su rika zuwa su na karɓar katikan su na zaɓe kafin babban zaɓe.
Ya kuma kara da cewa a aikin rijistar da aka kammala, an yi wa sabbin masu zaɓe 569,103 a jihar.