Home Labarai Akwai kwanciyar hankalin yin kasuwanci a Nijeriya — Lai Mohammed

Akwai kwanciyar hankalin yin kasuwanci a Nijeriya — Lai Mohammed

0
Akwai kwanciyar hankalin yin kasuwanci a Nijeriya — Lai Mohammed

 

 

 

 

Ministan yaɗa labarai da al’adu, Lai Mohammed, ya ce babu wata matsalar rashin tsaro ga kasuwanci a Nijeriya, duk da kamfe ɗin da ƴan adawar siyasa ke yi wa kasar.

Ministan ya bayyana hakan ne a wani bikin baje kolin masu saka hannun jari mai taken “Africa Walk”, wanda kungiyar UNICORN ta shirya a harabar ta ta Legas a yau Juma’a.

Masu kashewa ƙasar kasuwa kuma na nan na yaɗa labaran ƙarya da ƴan kasuwar ke yadawa cewa Nijeriya na cikin yaƙi ko kuma a na tauye hakkin yin addinai.

Mohammed ya ce gwamnatin Buhari ta hau mulki ne a shekarar 2015 da alkawarin gyara tattalin arziki, yaki da rashin tsaro da kuma dakile cin hanci da rashawa kuma gwamnatin ta taka rawar gani a kan alkawura ukun nan.

“An zabe mu ne a kan ginshikan tattalin arziki guda uku, tsaro, da yaki da cin hanci da rashawa. A cikin wadannan wurare uku, ina tabbatar da cewa duk mun cika alkawarin mu, duk da dimbin kalubalen da ake fuskanta,” in ji shi.

Yayin da yake magana kan tsaro, Ministan ya ce Boko Haram da ke rike da yankuna masu yawa a yankin Arewa maso Gabas kafin zuwan wannan Gwamnati ta fara tasamma zama tarihi sosai kuma an kawar da shugabancin ISWAP.

Ya ce ‘yan tada kayar bayan dubu 51 ne suka mika wuya a cikin watanni uku na farkon wannan shekarar kadai, yayin da a yanzu gwamnati ta maida hankali wajen gyarawa da sake gina al’ummomin da ‘yan ta’addan suka ɗaiɗaita.